Sahel

Rikici ya raba mutane fiye da miliyan 2 da muhallansu a Sahel

Wasu 'yan gudun hijira a yankin Sahel da rikici ya raba da muhallansu a sansanin Pissila, dake Burkina Faso. 13/11/2019.
Wasu 'yan gudun hijira a yankin Sahel da rikici ya raba da muhallansu a sansanin Pissila, dake Burkina Faso. 13/11/2019. Marwa Awad/WFP/Handout via REUTERS

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR, tace yanzu haka akwai mutane fiye da miliyan 2 da rikici ya raba da muhallansu a kasashen yankin Sahel.

Talla

Mai magana da yawun hukumar ta UNHCR Boris Cheshirkov ya ce adadin shi ne mafi yawa na mutanen da rikici ya raba da muhallansu a yankin, inda ya bukaci daukar matakin gaggauta kawo karshen matsalar.

Cheshirkov ya ce sassan yankin na Sahel da matsalar gudun hijirar tayi kamari sun hada sa yankunan Burkina Faso, Chadi, Mali da kuma Nijar.

Kakakin hukumar kula da ‘yan gudun hijirar ta duniya ya bukaci gaggauta tallafawa kasashen da matsalar ta shafa, la’akari da yadda tashe-tashen hankula da hare-haren ‘yan bindiga suka tilasta rufe makarantu, da kuma asibitocinsu da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.