Masar - RSF

RSF ta bukaci sakin wasu 'yan jaridu biyu a Masar

Kungiyar kare hakkin 'yan jaridu ta duniya RSF
Kungiyar kare hakkin 'yan jaridu ta duniya RSF AFP/Bertrand Guay

Kungiyar dake karę hakkokin Yan Jaridu ta Duniya RSF ta bukaci gwamnatin Masar da ta saki wasu Yan Jaridu guda 2 da suka bata makwanni biyu da suka gabata, wadanda ake zargi da yada labaran karya.

Talla

Kungiyar tace Hamdi al-Zaeem mai daukar hoto da Ahmed Khalifa editan wata jarida da ake wallafawa a intanet sun bata ne a ranakun 4 da 6 ga watan nan, bayan da jami’an tsaro suka kai hari gidajen su.

Daraktar RSF dake kula da Gabas ta Tsakiya Sabrina Bennoui tace bacewar Yan Jaridun biyu ya dada fito da irin hadarın da manema labarai ke fuskanta a Masar.

Kasar Masar ce kasa ta 166 daga cikin kasashen duniya 180 da ake take hakkin yan Jaridu, kuma yanzu haka ta daure sama da 30.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.