Birtaniya - Sudan

Sudan zata samu agajin Dala miliyan 55 daga Birtaniya

Wasu Sojin Sudan.
Wasu Sojin Sudan. Reuters

Kasar Birtaniya ta bayyana shirin baiwa Sudan agajin Dala miliyan 55, tare da baiwa Bankin Raya kasashen Afirka Dala miliyan 455 kudaden da ake bin sa.

Talla

Sakataren harkokin wajen kasar Dominic Rabb ya sanar da matakin a ziyarar da ya kai Khartoum, wadda itace ziyara ta farko da wani babban jami’in gwamnatin Birtaniya ya kai kasar a cikin sama da shekaru 10.

Rabb ya sanya hannu kan yarjejeniyar aiki tare da ministan Sudan domin zubawa talakawa kudin da ya kai Dala miliyan 55 wanda ake saran iyalai sama da miliyan guda da rabi su amfana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.