Afrika

Ana zargin Gwamnatin Guinee da kisan wasu yan Adawa

Alpha Condé Shugaban kasar Guinee
Alpha Condé Shugaban kasar Guinee RFI/Carol Valade

Amurka da kungiyar tarrayar Turai sun bayyana takaicin bayan samun labarin mutuwar wasu yan adawa biyu ga Shugaban kasar Guinee Alpha Conde a kurkuku na kasar ta Guinee.

Talla

Mamadou Ourou Bary ya rasu ne ranar 16 ga watan janairu a gidan yarin Conakry,wanda ake tsare da shit un ranar 5 ga watan Agusta na shekarar da ta shude.

Marigayin , memba ne na jam’iyyar UFDG a karkashin jagoran yan adawa Cellou Dalein Diallo.

Na biyu da ya rasa ran sa a kurkuku shine Roger Bamba da ya rasu a watan Disemba da ya shude kafin a gabatar da shi gaban alkali,wanda kuma gwamnati ta bayyana cewa ya na rasu ne bayan fama da rashin lafiya.

Kungiyar kare hakokin bil Adam ta amnesty na Allah wadai da cin zarafin yan adawa daga gwamnatin shugaba Alpha Conde.

Yan adawa na ci gaba da kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.