Najeriya

Gwamnan Zamfara ya koka dangane da halin tsaro a jihar

Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle
Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle premiumtimesng

A Najeriya,Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle ya zargin wasu shugabanin al’umat da suka hada da sarakuna da yiwa shirin samar da zaman lafiya da tsaro a yankin kafar ungulu.Gwamna Matawalle ya fadi haka ne yayin wani taro da shugabanin rundunonin tsaro na yankin ranar alhamis da ta gabata.

Talla

Gwamnan Zamfara a fusace ya kalubalanci sanarwar shugaban majalisar sarakunan galgajiya, daga cikin hukumomin galgajiyar yankin, sarkin Anka da ya bukaci hukumomi sun baiwa jama’a damar mallakar bindigogi don kare kan su, ganin gwamnati ta kasa shawo kan wannan matsalla.

A karshe gwamna Matawalle ya ce lamarin tsaro ya tabarbare a yankin ga baki daya da ma wasu yankunan Najeriya, to aman nauyi ya rataya wuyan kowane daga cikin mazauna kauyuka da birni da kuma ya dace sun dafawa jami’in tsaro da bayyanai a duk kowane lokaci .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.