Dubban masu zanga-zanga a Tunisia sun bijirewa dokar kulle
Wallafawa ranar:
Dubban matasa a Tunisia sun cigaba da mamaye titunan biranen kasar, inda suke zanga-zangar kyamar cin zarafin da ‘yan sanda ke musu, sai kuma tuhumar gwamnati da gazawa wajen magance matsalolin talauci da rashawa.
Mako guda kenan dubban matasan Tunisia suka shafe suna zanga-zangar adawa da gwamnati, inda suka rika yin arrangama da ‘yan sanda, duk da cewar gwamnati ta kafa dokar hana fitar dare daga 8 zuwa karfe 5 na asubah don dakile yaduwar annobar Korona da kawo yanzu ta halaka 'yan kasar sama da dubu 6.
Kawo yanzu daruruwan mutane ke tsare daga cikin masu zanga-zangar da jami’an tsaro suka kame tun daga ranar 14 ga watan nan.
A makon jiya al’ummar Tunisia suka cika shekaru 10 da yin juyin juya halin da ya kawar da gwamnatin marigayi Zine El Abidine Ben Ali a shekarar 2011, da suka tuhuma da mulkin kama karya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu