Muhalli

Guguwar Eloise ta tafka barna a Mozambique

Yadda guguwar Idaita mamaye yankunan birnin Beira na kasar Mozambique, a watan Maris na 2019.
Yadda guguwar Idaita mamaye yankunan birnin Beira na kasar Mozambique, a watan Maris na 2019. REUTERS/Siphiwe Sibeko/File Photo

Jami'an agaji a Mozambique sun dukufa wajen aikin ceto, bayan da kakkarfar guguwa dauke da ruwan sama ta afkawa birnin Beira dake gabar teku.

Talla

Kawo yanzu babu rahoton hasarar rai, sai dai rusa gine-gine da dama da guguwar tayi wadda masana suka wa lakabi da Eloise.

Masana yanayi sun ce guguwar na tsala gudun kilomita 160 a sa’a 1.

Shekaru biyu da suka gabata dai guguwar Idai ta tafka mummunar barna a garin na Beira dake gabar ruwa, inda ta salwantar da rayukan mutane da dama da kuma janyo hasarar dimbin dukiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.