Najeriya

Gwamnonin yammacin Najeriya na ganawa da shugabannin Fulani makiyaya

Gwamnonin kudu maso yammacin Najeriya.
Gwamnonin kudu maso yammacin Najeriya. NAN

Yau gwamnonin yammacin Najeriya ke gudanar da wani taro da shugabannin kungiyar Fulani makiyaya sakamakon tankiyar da ta biyo bayan umurnin ficewar su daga Jihar Ondo kamar yadda Gwamnatin Jihar ta basu umurni cikin mako guda.

Talla

Rahotanni sun ce yanzu haka shugabannin kungiyar Miyetti Allah sun isa Akure domin halartar taron wanda zai samu halartar Gwamnonin Jigawa da Kebbi da kumą kwamishinonin Yan Sandan dake Yammacin Najeriya.

Sakatare Janar na kungiyar Meyetti Allah Baba Usman Ngelzerma ya tabbatarwa RFI Hausa isar su Akure yammacin jiya, domin halartar taron.

Umurnin da aka Aiwa Fulanin na ficewa daga Jihar Ondo da kuma harin da aka Aiwa Sarkin Fulani a Jihar Oyo sun tada hankalin jama’a inda aka dinga samun musayar zafafan kalaman dake iya raba kań jama'a’r Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.