Buhari ya nada sabbin manyan hafsoshin tsaron Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da hafsoshin tsaron kasar.
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya da hafsoshin tsaron kasar. Punch

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da murabus din daukacin manyan hafsoshin sojin kasar inda ya maye gurbin su da wasu sabbi.

Talla

Sanarwar da mai ba shi shawara a fannin yada labarai Femi Adeshina ya raba wa manema labarai ta ce, Buhari ya amince da nadin Manjo Janar Leo Irabor a matsayin Hafsan Hafsoshin tsaro, yayın da Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya zama shugaban sojin kasa, sai kuma Rear Admiral A.Z. Gambo a matsayin shugaban sojin ruwa tare da Air Marshall I.O Amao a matsayin shugaban sojin sama.

Wadannan hafsoshin za su maye gurbin Janar Abayomi Olonisakin da Janar Yusuf Tukur Buratai da Air Marshal Abubakar Sadiq da kuma Vice Admirał Ibok Ekwe Ibas.

Shugaban kasar ya taya sabbin hafsoshin murna, yayın da ya gode wa wadanda suka yi ritaya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.