Kenya-Somalia

Mutane 11 sun mutu a rikicin da ya barke akan iyakar Kenya da Somalia

Wasu sojojin kasar Kenya
Wasu sojojin kasar Kenya Reuters

Akalla mutane 11 suka rasa rayukan su sakamakon wani tashin hankalin da aka samu a garin Baled-Hawo a yankin Jubaland dake iyakar Somalia da Kenya, yayin da wasu 11 kumą suka jikkata.

Talla

Rahotanni sun ce fadan ya barke ne daren ranar lahadi zuwa safiyar litinin, yayin da gwamnatin Somalia ta zargi gwamnatin Kenya da goyawa ‘yan tawaye baya domin kai hare hare a yankin.

Ya zuwa yanzu gwamnatin Kenya bata ce komai ba kan zargin.

Kenya dai ta dade tana goyon bayan Ahmed Madobe shugaban yankin na Jubaland mai kwaryakwaryar ‘yanci, wanda a yanzu dangantaka tayi tsami tsakaninsa da gwamnatin Somalia, abinda ya sanya shi kauracewa zabukan kasar dake shirin gudana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.