Bakin-Haure

MDD na bukatar dala miliyan 100 don kyautata rayuwan masu tsarewa daga Afirka zuwa Turai

Bakin haure da aka ceto a gabar ruwan Meditareniya
Bakin haure da aka ceto a gabar ruwan Meditareniya REUTERS/Borja Suarez

Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da bukatar miliyan dari na dala don agaza wa ‘yan gudun hijira da bakin haure dake tsallakawa zuwa Turai, ta hanyoyi masu hatsari don kauce wa yake yaken da ke ta’azzara a nahiyar Afrika.

Talla

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana matukar damuwa kan yadda rikice rikice ke ci gaba da daidaita al’umma daga yankin Sahel da kuma gabashin nahiyar ta Afrika.

Wannan ne abin da ke ingiza karin mutane yin kokarin jefa rayuwarsu cikin hatsari, ta wajen yunkurin ketare tekun Mediterranean don shiga nahiyar Turai, lamarin ya janyo mutuwar akalla mutane dubu 1 da 64 a shekarar da ta gabata.

A wata sanarwa, hukumkar kulada ‘yan gudun hijirar ta ce, kimanin dala miliyan 100 ne kawai take nema, don inganta kariyar ga ‘yan gudun hijira daga kasashen Afrika, wadanda a kulla yaumin ke kokarin ketare teku a cikin yanayi mai matukar hadari, tana mai cewa samar musu da zabi mafi inganci shi ne abu mafi a'ala a gareta.

Alkalumman Majalisar Dinikin Duniya na nuni da cewa, rikice rikice a yankin Sahel, da suka shafi kasashen Senegal Mauritania, Mali, Burkina Faso, Nijar, Najeriya Chad da Sudan, sun tilasta wa kimanin mutane miliya 2 da dubu dari 9 arcewa daga gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.