Afrika

Ta nemi ta danfare ni -Aliko Dangote

Aliko Dangote tareda Autumn Spikes
Aliko Dangote tareda Autumn Spikes RFI Hausa

Attajiri Aliko Dangote ya bukaci wata kotu dake Amurka da ta shiga tsakanin sa da tsofuwar budurwar sa Autumn Spikes wacce yanzu haka ke amfani da kafaffen sadarwa tareda wallafa wasu daga cikin hotunan ta tareda Aliko Dangote.

Talla

Autumn Spikes Wannan mata ta bayyana cewa sun share kusan shekaru 10 tare Aliko Dangote a matsayin budurwarsa.

A wani labarin wannan mata ta wallafa wani bidiyon ta tareda attajirin Aliko Dangote,sai yanzu haka Dangote ya bayyana cewa ta yi kokarin danfarar sa milyan biyar na dalla kudin Amurka, ta kuma yi amfani da haka cewa indan har ba ta samu biyan bukata ba ,za ta wallafa wasu daga cikin hotunan da suke tare.

Autumn Spikes ta ce za ta bi hanyoyin da suka dace don kwato hakkokin ta karma dai yada dokokin kasar da suke ciki suka shifuda. Spikes ta ce Attajirin ya yi mata tayin kudi da nufin ta rufe maganar alakarsu.

Kalo ya koma bangaren kotu yanzu haka,inda ake sa ran za su bayyana 9 ga watan Fabarairu shekarar 2021.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.