MDD ta gargadi Afrika kan yiwuwar barinta a baya a rigakafin Covid-19
Wallafawa ranar:
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewar kasashen Duniya sun yiwa Afirka fintinkau a kokarin da suke na ceto rayukan al’ummomin su daga cutar korona wajen basu allurar rigakafi.
Sakatare Janar na Majalisar Antonio Guterres ya ce abin takaici ne ganin yadda aka bai wa mutane sama da miliyan 70 allurar amma kuma wadanda suka samu a Afirka basu wuce dubu 20 ba.
Guterres ya bukaci kara kaimi daga kowanne bangare wajen ganin an yi allurar rigakafin tare ba tare da wani bangare a baya ba, abinda zai sa cutar ta kara jajircewa wajen bijirewa maganin da ake yakar ta.
Sakataren ya ce Duniyar na bukatar aikin hadin kai wajen ganin kowa ya samu allurar a lokaci guda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu