AU

Dole a sake fasalin kungiyar Tarayyar Afrika don ta yi tasiri - Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. Twitter@BashirAhmaad

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya zama dole a yi wa kungiyar kasashen Afirka ta AU garambawul domin ba ta damar sauke nauyin da ke kanta na kare martaba da kimar mutanen nahiyar baki daya.

Talla

Yayin da ya ke jawabi wajen taron shugabannin kungiyar karo na 34 da aka yi a karshen wannan makon, shugaba Buhari ya ce rashin daukar matakan yi wa kungiyar gyaran fuska zai dakushe kimar ta a idan duniya.

Buhari ya yaba wa shugaban Rwanda Paul Kagame wanda ya jagoranci kwamitin da ya gabatar da rahotan bukatar yi wa kungiyar garambawul, yayin da kuma ya gode wa shugabannin nahiyar saboda goyon bayan da suka bai wa Ambasada Bankole Adeoye, dan Najeriya wajen zama kwamishinan siyasa da tsaro da kuma tabbatar da zaman lafiya na kungiyar.

Sanarwar da mai taimaka masa ta bangaren yada labarai Garba Shehu ya raba wa manema labarai ta ce shugaban Najeriyar ya kuma taya shugaban gudanarwar kungiyar Moussa Faki Mahamat na Chadi murnar sake zaben sa domin yin wa’adi na biyu tare da mataimakiyar sa Dr Monique Nsanzabaganwa ta kasar Rwanda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI