Duniya

Afirka ta bukaci karin Dala biliyan 500 daga hukumar bada lamuni

Tambarin hukumar bayar da lamuni na Duniya
Tambarin hukumar bayar da lamuni na Duniya REUTERS/Yuri Gripas/File Photo

Kasashen Afirka sun bukaci karin Dala biliyan 500 daga Hukumar Bada lamuni ta duniya da kuma jinkirta karbar bashin da ake bin su domin shawo kan matsalolin da annobar korona ta haifar musu.

Talla

An gabatar da wannan bukatar ce lokacin da ministocin kudade daga nahiyar Afirka suka gudanar da taro a karkashin Hukumar Tattalin Arzikin Kasashen nahiyar da kuma Hukumar Bada Lamuni ta duniya.

Hukumar bada lamunin tace asusun da kasashen Afirka ke bukatar basu wadannan kudade har Dala biliyan 500 an kirkire shi ne a shekarar 1969 domin tallafawa asusun ajiyar kasashen dake cikin Hukumar.

Ya zuwa yanzu an baiwa kasashen Dala biliyan 281 domin tinkarar matsalolin da suka adadbe su.

Shima bankin Duniya ya bukaci kasashen dake cikin kungiyar G20 da su taimakawa kasashen masu tasowa wajen amfani da kudaden wajen fuskantar kalubalen da annobar korona ta haifar domin kare lafiyar jama’ar su.

Ya zuwa yanzu kasashen Duniya 73 suka cacanci daga musu kafa wajen jinkirta karbar bashin da ake abin su saboda matsalar da annobar ta haifar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI