Mali

Dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD a Mali 20 suka jikkata a wani harin yan ta'adda

Dakarun rundunar Sojin kasar Mali  FAMA (a Gao,  July 24, 2019
Dakarun rundunar Sojin kasar Mali FAMA (a Gao, July 24, 2019 AFP/Souleymane Ag Anara

Dakarun majalisar dinkin Duniya 20 ne suka jikata a kasar Mali sakamakon wani harin da aka kaiwa barikinsu a safiyar yau Laraba, a yankin Kerena, yankin na fama da hare haren yan ta’ada, kamar yadda kakakin rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar dinkin duniya a kasar Mali (Munisma) ya sanar

Talla

Barikin da aka kai wa harin na wucin gadi ne da ke Kerena kusa da Duwenza , da misalin  karfe 7 na safe ne hare haren suka soma da harbin rokoki, kafin ayi ta jin karar bindigogi masu sarrafa kansu, inji kakakin Munisma Olivier Salgado.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, sakamakon wucin gadi ya nuna cewa, sojoji 20 ne suka jikata kuma yawancinsu yan kasar togo ne dake aikin wanzar da zaman lafiya a kasar ta Mali.

Wasu daga cikinsu kuma sun samu munanan raunuka, shugaban rundunar ta Minusma, Mahamat Saleh Annadif, ya yi Allah waddai da harin, wanda ya ce na miyagun mutane ne da basu son zaman lafiya.

Ko a watan Jnairun jiya, sojoji 5 ne aka kashe sakamakon taka nakiya da motarsu ta yi.

Alkaluma dai na cewa rundunar Minusma itace rundunar majalisar dinkin duniya da ta fi samun asarar rayukan dakaru a tarihi, a makon jiya ma dai, wasu dakarun kasar Mali 10 sun rasa ransu a yankin Boni, bayan hari kan barikinsu, a yankin da kungiyar GSIM da ke kawance da AlQaida ta kaddamar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI