Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

Touadera ya tsaida ranar karasa zaben 'yan majalisar Jamhuriyar Afrika

Shugaban Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Faustin Archange Touadera bayan kada kuri'a a zaben shugaban kasa da ya gudana a ranar 27 ga watan Disamba na 2020.
Shugaban Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya Faustin Archange Touadera bayan kada kuri'a a zaben shugaban kasa da ya gudana a ranar 27 ga watan Disamba na 2020. REUTERS/Antonie Rolland/File Photo

Shugaban Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, Faustin Archange Touadera, yace zaben ‘yan majalisar kasar zagaye na biyu, zai gudana cikin wata mai kamawa a wasu mazabu, zalika za a karasa zaben zagaye na farko da ya gamu da cikas sakamakon tashe tashen hankula a watan Disambar bara.

Talla

Shugaba Touadera yace zabukan za su gudana a ranar 14 ga watan Maris, yayin da kuma za a soma yakin neman zaben na karashen zagayen farko a ranar 27 ga watan nan Fabarairu, sai kuma 6 ga watan Maris ranar soma yakin neman zaben yan majalisar na zagaye na 2.

Alkalumma sun nuna cewar kimanin kashi 1 bisa 3 na jumillar kuri’u kawai aka samu kadawa yayin zaben shugaban kasa dana ‘yan majalisa da ya gudana a ranar 27 ga watan Disamba, saboda hare haren 'yan tawaye a yankunan dake karkashin ikonsu.

Sai dai duk da haka a watan Janairu babbar kotun kasar ta Jamhuriyar Afrika ta tabbatar da nasarar shugaba Touadera da ya lashe zaben, bayan samun kashi 53.16 na yawan kuri’un da aka kada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI