Shuaibu Liman a kan zargin kafofin yada labarai da ruruta rikici a Najeriya

Sauti 04:00
wasu 'yan sandan ciki na DSS a Najeriya.
wasu 'yan sandan ciki na DSS a Najeriya. venturesafrica

A makon da ya gabata ne wani rikicin kabilanci ya tashi tsakanin Yarabawa da Hausawa a kasuwar Sasa dake jihar Oyo a Najeriya, lamarin da ya yi sanadin barnar rayuka da dukiyoyi.Sai dai an yi ta nuna wa kafofin yada labarai da na sadarwar zamani yatsa a kan ruruta wutar rikicin, inda ake ganin da dama sun saki layi, sun hau dokin zuciya, suka yi ta yada labarai masu tada hankali.A ka haka ne Michael Kuduson ya tattauna da sakataren kungiyar ‘yan jarida ta Najeriya, Malam Shuaibu Liman, wanda ya fara bayani kamar haka: