Kamaru: mutane 5 sun mutu, 51 sun jikkata a hatsarin safa
Wallafawa ranar:
Rahotanni daga Kamaru sun ce akalla mutane 5 suka mutu, cikin su har da da jariri mai wata 9, yayin da wasu 51 suka jikkata sakamakon hadarin motar safa a yammacin kasar a daren Litinin.
Gwamnan Awa Fonka Augustine ya ce wannan hadarin ya auku ne lokacin da motar safar dauke da fasinjoji ta kauce hanya inda tayi ta mirginawa a akan hanyar Koutaba zuwa Yaounde.
Daga cikin mutane 51 da suka samu raunuka, 15 daga cikin su raunin nasu yayi tsanani sosai.
Ko a watan jiya mutane 53 suka mutu lokacin da motar da suke ciki ta yi taho - mu gama da motar daukar mai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu