Italiya-Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo

Jamhuriyar Congo ta dora alhakin kisan jakadan Italiya kan 'yan tawayen Hutu

Mayakan 'yan tawayen Hutu na Rwanda.
Mayakan 'yan tawayen Hutu na Rwanda. AFP / HOCINE ZAOURAR

Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo ta zargi ‘yan tawayen Hutu na Rwanda da kaddamar da farmakin da ya halaka jakadan Italiya a kasar da wasu mutum biyu Litinin din nan.

Talla

Tun farko ‘yan bindigar da gwamnatin Congo ta bayyana da mayakan ‘yan tawayen Hutu na Rwanda ne suka yiwa tawagar hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya kwantan bauna, cikin tawagar kuwa har da jakadan na Italiya Luca Attanasio wanda ya rasa ransa hade da dogarin da ke bashi tsaro dan Italiya kana Direbansa da ba a bayyana ko na ina ne ba.

Sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen Congo ta fitar ta ce ‘yan tawayen sun kuma yi garkuwa da mutum 4 cikin tawagar ko da ya ke an gano daya yanzu haka bayan bin sahunsu.

Jakadan na Italiya Attanasio mai shekaru 43 shi ne matashin jami’in Diflomasiyyar kasar da ke da kyakkyawar manufa a nahiyar Afrika inda ya fara wakiltar kasarsa a Kinshasa tun 2017, yayinda ya fara aikin jakadanci a 2019.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake kashe jakadan wata kasa ta Turai a Jamhuriyyar Congo ba, domin kuwa ko a shekarar 1993 sai da jakadan Faransa Philippe Bernard ya rasa ransa a wani yamutsin adawa da tsohon shugaban kasar Mobutu Sese Seko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.