Najeriya da Guinea sun kulla yarjeniyoyi a bangaren man fetur

Daya daga cikin matatun man fetur a Najeriya.
Daya daga cikin matatun man fetur a Najeriya. Africanews

Wakilan Ma’aikatar Albarkatun Man Fetur ta Najeriya sun gudanar da taron hadin gwiwa da takwarorinsu Equatorial Guinea a Malabo.

Talla

Ministan ma’adanai da albarkatun kasa na Equatorial Guinea, Gabriel Mbaga Obiang Lima, ya karbi bakunci takwaransa na  Najeriya Timipre Sylva, a fadar shugaban kasa da ke Malabo da nufin karfafa alakar kasashen biyu.

Ministocin biyu sun sanya hannu a kan yarjejeniyar fahimtar juna, wanda zai karfafa sabbin damammaki ga bangaren albarkatun mai na kasashen biyu masu arzikin Man Fetur a duniya.

Haka zalika, kasashen biyu, sun amince da hada kai kan dabarun yakar fashin teku, a yayin da tsaro ya kasance babban abin damuwa ga samar da makamashi, a dai-dai lokacin da  fashin teku ke kara ta’azzara a tekun Gulf na Guinea.

Ministocin sun kuma amince da hadin gwiwar samar da iskar gas daga Najeriya zuwa Equatorial Guinea wanda kuma zai zama wata dama ga bangaren makamashin Equatorial Guinea ta bunkasa shirin samar wa ‘yan kasarta abubuwan more rayuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.