Guinea-Ebola

Guinea ta kaddamar da shirin baiwa jama'a rigakafin Ebola

Wasu jami'an Lafiya da ke shirin tunkarar aikin rigakafin na Ebola.
Wasu jami'an Lafiya da ke shirin tunkarar aikin rigakafin na Ebola. REUTERS/Baz Ratner/File Photo

Gwamnatin Kasar Guinea ta kaddamar da shirin fara bai wa jama’arta allurar rigakafin cutar Ebola sakamakon sake samun bullar cutar a sassan kasar.

Talla

Hukumar lafiya ta duniya da ta kasar sun ce an fara gabatar da allurar ce a Gouecke bayan kasar ta karbi alluran dubu 11,000 a ranar litinin din da ta gabata, bayan tun farko jirgin da ke dauke da alluran daga Amurka ya gaza sauka kasar saboda hazo.

Ministan lafiyar kasar Remy Lamah tare da wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya sun ziyarci yankin domin sanya ido akai.

WHO ta sanar da cewa daga kasar ta Guinea ne za a faro rigakafin gabanin fadada shi zuwa Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo bayan sake samun masu dauke da cutar cikin kasar.

Tuni dai tawagar kwararrun lafiya ta WHO da ke ofishinta na Afrika suka kammala hallara a Guinea don tunkarar yaki da cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI