Congo-Hutu

'Yan tawayen Hutu sun musanta kisan Jakadan Italiya a Jamhuriyar Congo

Wasu mayakan 'yan tawayen Hutu a Congo.
Wasu mayakan 'yan tawayen Hutu a Congo. Reuters/James Akena

'Yan Tawayen Hutu da ke kasar Rwanda sun nesanta kan su da harin da ya hallaka Jakadan Italia, yayin da suka zargi sojojin Jamhuriyar Demokiradiyar Congo da na Rwanda da aikata kisan.

Talla

Ma’aikatar cikin gidan Congo ta zargi 'yan Tawayen FDLR da ke Rwanda da kashe jami’in, amma 'yan Tawayen sun musanta zargin kai tsaye.

'Yan tawayen sun ce an kashe Jakadan ne kusa da iyakar Rwanda, saboda haka sojojin kasashen biyu ke da alhakin kisan.

Tun a litinin din da ta gabata ne wasu 'yan bindiga suka farwa tawagar hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya tare da hallaka jakadan na Italiya Luca Attanasio da dogarin da ke bashi tsaro dan Italiya kana Direbansa da ba a bayyana ko na ina ne ba.

Jakadan na Italiya Attanasio mai shekaru 43 shi ne matashin jami’in Diflomasiyyar kasar da ke da kyakkyawar manufa a nahiyar Afrika inda ya fara wakiltar kasarsa a Kinshasa tun 2017, yayinda ya fara aikin jakadanci a 2019.

Wannan dai ba shi ne karon farko da ake kashe jakadan wata kasa ta Turai a Jamhuriyyar Congo ba, domin kuwa ko a shekarar 1993 sai da jakadan Faransa Philippe Bernard ya rasa ransa a wani yamutsin adawa da tsohon shugaban kasar Mobutu Sese Seko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.