Kamaru

Sojojin Kamaru sun yi wa nakasassu fyade-HRW

Human Rights Watch ta ce, sojojin Kamaru sun yi wa mata da suka hada da nakasassu fyade a yankin masu magana da Turancin Ingilishi
Human Rights Watch ta ce, sojojin Kamaru sun yi wa mata da suka hada da nakasassu fyade a yankin masu magana da Turancin Ingilishi © AFP - Marco Longari

Kungiyar Kare Hakkin Bil'adama ta Human Rights Watch ta zargi sojojin Kamaru da laifin yi wa mata 20 da suka hada da nakasassu 4 fyade tare da kashe wani mutum guda, a wani samame da suka kai a yankin masu amfani da turancin Ingilishi da ke neman ballewa daga kasar.

Talla

Kungiyar ta Human Rights Watch ta ce, harin da aka kai kauyen Ebam da ke kudu maso yammacin kasar shi ne mafi muni da sojojin kasar suka kai a cikin shekaru 4 da suka  kwashe suna jan daga da ‘yan aware.

Bayan ta gana da wadanda suka tsallake rijiya da baya, kungiyar ta fitar da wata sanarwa da ke cewa, mayakan gwamnati sun yi wa maza kawanya, yayin da wasu daga cikinsu suka yi wa mata 20 da suka hada da nakasassu 4 fyade.

An rawaito daga ganau  cewa, fiye da sojoji 50 ne suka yi wa kauyen Ebam dirar mikiya kafin wayewar garin ranar 1 ga watan Maris ta shekarar da ta gabata, bisa zargin cewa al’ummar kauyen na bai wa dakarun ‘yan aware hadin kai, har ma da ba su matsuguni.

A shekarar 2017 ne wasu tsageru a  yankin masu amfani da turancin Ingilishi na Kamaru suka ayyana ‘yancin kai bayan korafin cewa, yankin masu amfani da Faransanci na nuna musu wariya, sai dai kasar Ambazonia da suka ayyana, ba ta samun goyon bayan kasashen duniya ba, kuma gwamnatin Kamaru ta mayar da martani da karfin bakin bindiga.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.