Afrika ta Kudu

Afrika ta Kudu ta janye dokar takaita walwala saboda ceto tattalin arziki

Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa
Shugaban kasar Afrika ta kudu Cyril Ramaphosa - World Health Organization/AFP

Shugaban Africa ta kudu Cyril Ramaphosa ya sanar da shirin sassauta dokar takaita zirga-zirga da kasar ke fuskanta tun bayan tsanantar coronavirus da ta tilasta takaita walwalar jama’a don dakile cutar.

Talla

Shugaba Ramaphosa wanda ya bayyana hakan ta cikin wani jawabi da ya yi ta kafar talabijin din kasar, ya ce takaita dokar wadda ta fara aiki tun tsakar daren jiya za ta bayar da damar ci gaba da hada-hadar kasuwanci, a dai dai lokacin da kasar ke cikin matsanancin halin tattalin arziki.

Ramaphosa yace an dauki wannan mataki ne bayan da aka fara samun raguwar yaduwar cutar tsakanin jama’a a kasar, bayan da aka sami adadin mutane dubu 10 cikin makon da ya gabata, kasa da dubu 40 da aka samu cikin makkonni biyu da suka gabata kenan.

Ya ce an sami wannan nasara ne bayan da hukumomi da jami’an lafiya suka kara kaimi wajen yaki da cutar, inda yace a yanzu dokar takaita zirga-zirgar zata fara aiki ne daga karfe 12 na dare zuwa 4 na asuba.

Ya zuwa yanzu dai kasar na da yawan mutane sama da miliyan 1 da rabi da ke fama da cutar, inda aka yiwa jami’an lafiya kusan dubu 63 da dari 6 rigakafin cutar, yayin da nan gaba kadan za’a fara yiwa jama’ar gari.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.