Habasha

Sojin Habasha sun saki ma'aikatan Jarida 4 da suka kame a yankin Tigray

Yankin Tigray mai fama da rikicin 'yan tawaye.
Yankin Tigray mai fama da rikicin 'yan tawaye. Tiksa Negeri/Reuters

Rahotanni daga Habasha sun tabbatar da sakin wasu ma’aikatan jarida 4 da hukumomin kasar suka kame tun ranar Asabar din da ta gabata a yankin Tigray mai fama da rikicin 'yan tawayen TPLP da ke fafutukar samarwa yankin ‘yancin cin gashin kai.

Talla

Tun a Asabar din da ta gabata ne, sojin Habasha suka kame ma’aikatan hudu, ciki har da na kamfanin dillancin labaran Faransa 2 da kuma na Financial Times.

Sai dai AFP ta wallafa cewa da safiyar yau ta yi magana da ma’aikatanta biyu da aka kame kuma sun shaida mata cewa sun sake sub a tare da daukar wani mataki ba tun da safe.

Tun cikin watan Nuwamban 2020 yankin na Tigray ke fama da rikici bayan da Firaminista Abiy Ahmed ya yi umarnin fatattakar mayakan ‘yan tawayen yankin na TPLF bayan da ya zarge su da farmakar Sojin kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.