Afrika-Coronavirus

Shirin rigakafin Korona ya kan-kama a Afrika

Akwatin allurar rigakafin cutar coronavirus karkashin shirin Covax
Akwatin allurar rigakafin cutar coronavirus karkashin shirin Covax SIA KAMBOU AFP

Miliyoyin alluran rigakafin coronavirus da aka samar karkashin shirin Covax, sun isa Najeriya da Jamhuriyar Demokuradiyar Congo da Angola da Kenya, a daidai lokacin da kasashen Afrika ke kara kaimi  wajen yi wa jama’arsu rigakafin cutar.

Talla

Najeriya  wadda ke zama kasa mafi yawan al’umma a Afrika, ta  karbi allurai kimanin miliyan 4, yayin da Jamhuriyar Demokuradiyar Congo ta karbi miliyan 1.7, inda kuma Angola ta karbi sama da dubu 600, a daidai lokacin da Gambia ke dakon karbar dubu 30.

 

Gwamnatin Najeriya ta karbi alluran rigakafin coronavirus karkashin shirin Covax

 

Ita ma  Kenya ta karbi alluran na AstraZaneca karkashin shirin Covax  har guda miliyan 1.

A makon jiya ne Ghana da Ivory Coast suka zama kasashen Afrika na farko da suka fara karbar rigakafin  wanda aka samar da shi kyauta ga kasashen duniya  matalauta.

Tuni kasashen duniya mawadata suka yi nisa a shirin yi wa al’umominsu rigakafin cutar ta coronavirus, inda suka yi wa  kananan kasashe da dama fintinkau, abin da ya sa Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadin cewa, ba za a ci galabar wannan annoba ba har sai  kowacce kasa ta yi wa jama’arta rigakafin.

Sai dai har yanzu ana fuskantar kalubalen gudanar da shirin rigakafin a wasu tarin kasashen Afrika saboda matsalar kayayyakin more rayuwa da kuma tabarbarewar tsaro kamar yadda Faisal Shuaib, darekta a Hukumar Kiwon Lafiya ta Najeriya Matakin Farko ya bayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.