Ghana

Kotun Kolin Ghana ta yi watsi da karar neman soke zaben shugaban kasar

Tsohon shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama
Tsohon shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama AP - Gabriela Barnuevo

Kotun Kolin kasar Ghana ta yi watsi da karar da tsohon shugaban kasar John Dramani Mahama ya gabatar dangane da zaben shugaban kasar da aka yi ranar a 7 ga watan Disambar bara, wanda yake zargin cewar an tafka magudi.

Talla

Babban alkalin kotun Kwesi Anin Yeboah ya ce Mahama ya gaza wajen gabatar da shaidun dake tabbatar da cewar an tafka magudi a zaben, saboda haka basu da hurumin bada umurnin gudanar da sabon zabe kamar yadda ya bukata.

Mai shari’ar yace babu wata shaida ko kadan da tsohon shugaban ya gabatar da zai jefa shakku kan sakamakon zaben wanda ya nuna cewar shugaba Nana Akufo-Addo ya samu kashi 51.59 na kuri’un da aka kada, yayin da shi kuma ya samu kashi 47.36.

A zaben 'yan majalisun da aka yi kowacce daga cikin manyan Jam’iyyun kasar ta Ghana NDP da NPP ta samu kujeru 137 yayin da wani dan takara mai zaman kan sa ya lashe sauran kujerar.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.