Afrika-Coronavirus

Coronavirus ta fi kashe Maza fiye da takwarorinsu Mata a Afrika- MDD

Wasu iyalai yayin birne gawar da Coronavirus ta kashe a Afrika ta kudu.
Wasu iyalai yayin birne gawar da Coronavirus ta kashe a Afrika ta kudu. REUTERS - Sumaya Hisham

Majalisar Dinkin Duniya ta ce binciken masana ya bayyana cewar cutar corona ta fi kashe maza a Afirka maimakon mata, yayin da matan suka fi mutuwa wajen matsalolin da ke da nasaba da haihuwa tun bayan barkewar annobar a bara.

Talla

Binciken da aka gudanar a kasashe 28 da ke Afirka da suka hada da Guinea da Mauritius da kuma Uganda ya nuna cewar mata kadan ne suka kamu da cutar corona kuma suka mutu sabanin maza.

Rahotan ya ce kashi 41 na wadanda suka kamu da cutar a Afirka mata ne, duk da ya ke alkaluman sun banbanta tsakanin kasa zuwa kasa, inda a Jamhuriyar Nijar ake da kashi 31, sabanin kashi 57 da aka gani a Afirka ta kudu.

Daraktar Hukumar Lafiya da ke kula da kasashen Afirka, Matshidiso Moeti, ta ce a kasashe da dama mata basa mutuwa sakamakon harbuwa da cutar corona sabanin yadda maza ke mutuwa, yayin da annobar ta bankado irin matsalolin da kasashe ke fuskanta wajen harkokin kula da lafiya.

Moeti ta kuma ce an samu karuwar matan da ke mutuwa sakamakon matsalolin da suka shafi haihuwa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.