Eritrea-Habasha

Dakarun Eritrea sun kashe daruruwan fararen hula-HRW

Cikin garin Aksoum da ke kasar Eritrea
Cikin garin Aksoum da ke kasar Eritrea Creative commons/Jialiang Gao

Wani rahoton Kungiyar Kare hakkin bil’adama ta Human Right Watch na cewa dakarun Eritrea sun kashe daruruwan fararen hula har da kananan yara ‘yan kasar  a watan Nuwamba da ya gabata a yankin Tigray na kasar Habasha.

Talla

Wannan rahoto shi ne na biyu dan tsakanin nan da ke zargin dakarun Eritrea da cin zarafin ‘yan kasar a garin Axum mai dadadden tarihi wanda kuma Hukumar UNICEF ke kula da shi.

Binciken da kungiyar Amnesty ta gudanar na nuna yadda dakarun Eritrea suka yi ta kashe mutane ba Kan-gado a yankin, wanda ke zuwa a wani lokaci da hankulan duniya ke tashi game da mummunan rahoton muzguna wa mutane da dakarun Eritrea ke yi.

Shugabannin Majalisar Dinkin Duniya ta zargi dakarun Eritrea da laifukan yaki.

Firaministan  Habasha Abiy Ahmed ya sanar  tun watan Nuwamba da ya gabata, cewa za su sanya kafar wando daya da shugabannin Tigray, kuma sun yi haka ne saboda gayyatar su don taimaka wa sojan Eritrean.

 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.