Habasha-Tigray

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci ficewar Sojin Habasha daga yankin Tigray

Dakarun Sojin Habasha a yankin Tigray.
Dakarun Sojin Habasha a yankin Tigray. Reuters

Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci sojojin gwamnatin Habasha da su fice daga yankin Tigray mai fama da tashin hankali, bayan rahoto ya bayyana cewar sojojin sun aikata laifuffukan yaki.

Talla

Shugabar Hukumar kare hakkin Bil Adama Michelle Bachelet ta bukaci kafa kwamiti mai zaman kan sa domin gudanar da bincike kan lamarin.

Bachelet tace ofishin ta yayi nasarar samun shaidun dake tabbatar da wasu zarge zargen da ake yiwa sojin wajen amfani da manyan makamai a yankunan fararen hula.

Rahotan ya kuma zargi sojojin Eritrea da suka taimakawa Habashar da aikata irin wadannan laifuffuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.