Senegal-ECOWAS

ECOWAS ta bukaci kawo karshen tashin hankalin da ya barke a Senegal

Wasu daga cikin fusatattun magoya bayan Ousmane Sonko yayin arrangama da jami'an tsaro a birnin Dakar.
Wasu daga cikin fusatattun magoya bayan Ousmane Sonko yayin arrangama da jami'an tsaro a birnin Dakar. AP - Leo Correa

Kungiyar kasashen Afirka ta Yamma ta bukaci bangarorin dake rikici a Senegal da suyi taka tsan tsan, bayan kwashe kwanaki ana arrangama tsakanin jami’an tsaro da magoya bayan shugaban Yan adawa Ousmane Sonko.

Talla

Sanarwar da kungiyar ECOWAS ta bayar ya bukaci kwantar da hankali daga kowanne bangare da kuma bukatar gwamnati ta dauki matakan da suka dace wajen kawo karshen tankiyar da aka samu da kuma tababtarwa jama’a damar da suke da ita na gudanar da zanga zanga cikin lumana.

Magoya bayan jagoran 'yan adawar Senegal Ousmane Sonko, yayin zanga-zangar adawa da kame da jami'an tsaro suka yi.
Magoya bayan jagoran 'yan adawar Senegal Ousmane Sonko, yayin zanga-zangar adawa da kame da jami'an tsaro suka yi. AP - Leo Correa

Akalla mutane 4 suka mutu sakamakon barkewar zanga zangar da aka kwashe kwanaki anayi, bayan kama Sonko mai shekaru 46 da ake zargi da tinzira tashin hankali.

A ranar juma’a an dauki dogon lokaci ana arangama tsakanin masu zanga zangar da jami’an tsaro, abinda aka bayyana a matsayin tashin hankalin da ba’a taba gani ba a cikin‚ 'yan shekarun da suka gabata.

rahotanni sun ce masu zanga zangar sun kona motoci akan titunan Dakar da wasu muhimman gine gine tare da kwashe dukiyar dake cikin shagunan sayar da kaya mallakar wani kamfanin Faransa da kai hari makarantun Faransa,  abinda ya haifar da arangama tsakanin su da jami’an tsaro.

Daya daga cikin motar sojojin kasar Senegal yayin da suka isa birnin Dakar domin taimakawa 'yan sanda wajen tashin hankalin da ya barke tsakanin jami'an tsaro da daruruwan magoya bayan jagoran 'yan adawa Ousmane Sonko.
Daya daga cikin motar sojojin kasar Senegal yayin da suka isa birnin Dakar domin taimakawa 'yan sanda wajen tashin hankalin da ya barke tsakanin jami'an tsaro da daruruwan magoya bayan jagoran 'yan adawa Ousmane Sonko. AP - Sylvain Cherkaoui

Ana saran Sonko ya gurfana a kotun Dakar ranar litinin domin amsa zargin yin fyade.

Boren da magoya bayan Sonko ke yi ya kazance ne bayan da kotu a birnin Dakar ta bada umarnin cigaba da tsare maigidan nasu bayan zaman farko da ta yi kan tuhumar da ake masa na yiwa wata ma’aikaciyar shagon tausa fyade.

 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.