Kamaru - coronavirus

Kamaru zata karbi allaurar rigakafin korona sama da miliyan daya

Maganin rigakafin annobar korona da kamfanin Astarazeneca ya samar
Maganin rigakafin annobar korona da kamfanin Astarazeneca ya samar AP - Christophe Ena

Kasar Kamaru dake daya daga cikin kasashen Afirka da annaobar korona dafi addaba, ta sanar da shirin karbar allurar rigakafin cutar sama da miliyan daya nan ba da jimawa ba.

Talla

Firayinministan kasar Joseph Dion Ngute wanda ya sanar da haka jiya Juma'a, ta kafar radiyo ta Talabijin din kasar CRTV, bai bayyana nau’in allurar ba.

Dion Ngute ya yi kira ga jama'a da su yi rigakafin, da zaran gwamnatin ta kaddamar, ko da yake ya ce shirin rigakafin zai kasance ne bisa son rai babu tilas.

To sai dai Firayinministan ya nuna damuwa kan rashin bin dokokin hana yaduwar cutar da gwamnati ka kafa, masamman sanya takunkumin rufe hanci da baki a bainar jama’a da kuma hana tarukan mutane sama da 50.

Ngute yace, "a cikin mako guda, an samu sabbin kamuwa da cutar fiye da 3,000, wanda ya kawo adadin mutanen da suka kamu da cutar zuwa 38,988 a kasar.

Kamaru, mai yawan mutane miliyan 26, ta yi rajistar mutane 588 da suka mutu samakon harbuwa da cutar tun bayan bullarta zuwa yanzu.

Mista Dion Ngute ya kara da cewa, Iyakokin Kamaru, na kasa da na ruwa da kuma ta sama zasu kasance a rufe, saboda yakar cutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.