Ghana tayi bikin cika shekaru 64 da samun 'yancin kai daga Birtaniya

Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Ado lokacin bukin tunawa da samun yancin kai, a filin Yanci dake Accra, ranar 06 ga watan Maris shekarar 2021
Shugaban kasar Ghana Nana Akufo Ado lokacin bukin tunawa da samun yancin kai, a filin Yanci dake Accra, ranar 06 ga watan Maris shekarar 2021 © Ghana presidency

Kasar Ghana tayi bikin cika shekaru 64 da samun ‘yancin kai daga Turawan mulkin mallakar Ingila, sakamakon zaman kasar ta farko a Afirka da tayi watsi da mulkin mallaka a ranar 6 ga watan Maris na shekarar 1957.

Talla

Kamar yadda aka saba yau an gudanar da shagulgula da faretin soji domin tuna irin gwagwarmayar da shugabannin farkon suka yi na ganin kasar ta samu ‘yancin cin gashin kai.

A sakon shugaba Nana Akufo-Addo ga al’ummar kasar ya jinjinawa shugabannin Ghana na farko da suka budewa kasashen Afirka kofar samun yancin a matsayin kasa ta farko da kuma cigaba da rike tuta wajen tabbatar da cewar kowacce kasa a Afirka ta samu ‘yanci.

Shugaban Ghana Nana Akufo Ado, yayin bukin ranar samun yancin kai a filin tunawa da yanci dake Accra, ranar 06 ga watan Maris shekarar 2021
Shugaban Ghana Nana Akufo Ado, yayin bukin ranar samun yancin kai a filin tunawa da yanci dake Accra, ranar 06 ga watan Maris shekarar 2021 © Ghana presidency
Akufo-Addo ya bukaci jama’ar kasar da su cigaba da taka rawa wajen gina Ghana domin shimfida ginshiki mai dorewa da zasu baiwa masu zuwa nan gaba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.