Ivory Coast-Siyasa

Al'ummar Ivory Coast na dakon sakamakon zaben 'yan majalisar dokokin kasar

Wata 'yar kasar Ivory Coast yayin kada kuri'a a zaben kasar.
Wata 'yar kasar Ivory Coast yayin kada kuri'a a zaben kasar. ASSOCIATED PRESS - Schalk van Zuydam

Al'ummar Ivory Coast ‘yan majalisu a Ivory Coast, zabe na farko dake gudana, bayan na shugaban kasar aka yi a shekarar bara, wanda rikici ya biyo bayansa.

Talla

‘Yan takara fiye da dubu 1 da 500 suka fafata a zaben da ya gudana a ranar Asabar, inda suke neman shiga zauren majalisar dokokin kasar at Ivory Coast mai yawan kujeru 255.

A karon farko bayan shafe shekaru 10 tana kauracewa shiga takara a dukkanin zabuka, jam’iyyar 'Ivorian Popular Front' ta jagoran ‘yan adawa a yanzu kuma tsohon shugaban kasar Laurent Gbagbo ta tsaida ‘yan takara a zaben ‘yan majalisun dake gudana.

Yayin zaben 'yan majalisun dokokin na Ivory Coast a watan Disambar shekarar 2016, jam'iyyar RHDP ta shugaba mai ci Alassane Ouattara ce ta lashe mafi rinjayen kujeru da adadin 167, bayan kawancen da ta kulla da jam'iyyar adawa ta PDCI.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.