Faransa-Afrika

Faransa za ta karfafa alakarta da Afrika don dakile tasirin China a nahiyar

Shugaban Faransa Emmanuel Macron bayan tattaunawar kwamitin tsaron kasashen Faransa da Jamus ta hoton bidiyo
Shugaban Faransa Emmanuel Macron bayan tattaunawar kwamitin tsaron kasashen Faransa da Jamus ta hoton bidiyo Reuters

Gwamnatin Faransa ta ce shiri yayi nisa dangane da yiwa manufofinta a kasashen Afrika garambawul ta hanyar kara yawan tallafin da take basu, la’akari da yadda tasirin kasar China ke cigaba da karuwa cikin sauri a nahiyar ta Afrika.

Talla

Alkaluma sun nuna Faransa ta kara yawan kudaden da take warewa wajen tallafi da kuma hada-hadar cinikayya tsakaninta da kasashen Afrika duk shekara daga euro biliyan 10 da miliyan 9 zuwa euro biliyan 12 da miliyan 800 a shekarar bara, duk da tasirin annobar Korona.

Sai dai za a iya cewa har yanzu tsugunno ba ta karewa Faransar ba, domin kuwa a shekarar 2019 kididdiga ta nuna cewar hada-hadar cinikayya gami da tallafi tsakanin China da kasashen Afrika sun lakume euro biliyan 161, abinda ya sa ta zarta Amurka wajen karfafa alaka da nahiyar.

Wani rahoton asusun bada lamuni na duniya ya ce a shekarar 2019, Afrika ta zama nahiya mafi samun karuwar cigaba a fannoni da dama na tattalin arziki da yawan jama’a, inda kwararru suka yi has ashen cewar adadin yawan al’ummar nahiyar zai kai kimanin mutane biliyan 2 da miliyan 200 a shekarar 2050.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.