Senegal

Jam'iyyun adawar Senegal sun sha alwashin jagorantar zanga-zangar kwanaki 3

Masu zanga-zanga a birnin Dakar na kasar Senegal.
Masu zanga-zanga a birnin Dakar na kasar Senegal. AP - Sylvain Cherkaoui

Gamayyar jam’iyyun adawa a Senegal sun bukaci al’ummar kasar da su mara musu baya wajen gudanar da zanga-zangar adawa da gwamnati.

Talla

Yayin sanar da matakin ga taron menama labarai ta suka kira ranar Asabar a birnin Dakar, jam’iyyun adawar sun ce zanga-zangar da za a soma daga ranar Litinin, za ta shafe kwanaki uku tana gudana.

Tun ranar Larabar da ta gabata tashin hankali ya barke a Dakar babban birnin Senegal, bayan da jami’an tsaro suka kame jagoran ‘yan adawa Ousmane Sonko yayin da yake kan hanyar zuwa kotu don amsa tuhuma kan zargin aikata fyade.

Jami’an tsaron sun kame Sonko yayin da dauruwan magoya bayansa ke masa rakiya ne cike da bushe bushe, bisa zarginsa da tayar da hatsaniya, abinda ya janyo arrangamar da ta halaka akalla mutane 4.

Yadda wani sashin birnin Dakar ya yamutse sakamakon arrangama tsakanin magoya bayan Ousmane Sonko da jami'an tsaro.
Yadda wani sashin birnin Dakar ya yamutse sakamakon arrangama tsakanin magoya bayan Ousmane Sonko da jami'an tsaro. AP - Leo Correa

A ranar Juma’a an dauki dogon lokaci ana arrangama tsakanin masu zanga zanga da jami’an tsaro, abinda aka bayyana a matsayin tashin hankalin da ba’a taba gani ba a cikin 'yan shekarun da suka gabata.

Rahotanni sun ce masu zanga zangar sun kona motoci akan titunan Dakar da wasu muhimman gine gine tare da kwashe dukiyar dake cikin shagunan sayar da kaya mallakar wani kamfanin Faransa da kai hari makarantun Faransa,  abinda ya haifar da arangama tsakanin su da jami’an tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.