Equatorial Guinea

Mutane da dama sun mutu a Equatorial Guinea bayan fashewar sinadaran bam

Hoton bidiyo dake nuna yadda bakin hayaki ya turnuke a sansanin sojin kasar Equatorial Guinea dake birnin Bata.
Hoton bidiyo dake nuna yadda bakin hayaki ya turnuke a sansanin sojin kasar Equatorial Guinea dake birnin Bata. AP

Ma’aikatar lafiyar Equatorial Guinea ta ce mutane akalla 20 ne suka rasa rayukansu yayinda wasu fiye da 500 suka jikkata, sakamakon tarwatsewar nakiyoyi a sansanin sojin Nkoa Ntoma dake Bata, birni mafi girma a kasar.

Talla

Yayin jawabin da ya gabatar ta kafar talabijin jim kadan bayan aukuwar fashe-fashen a ranar Lahadi, shugaban kasar ta Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema, ya ce sakaci wajen kula da nakiyoyin dake ajiye a sansanin sojin na garin Bata ne ya janyo tashin hankalin.

Alkaluman ma’aikatar lafiyar kasar dai sun nuna cewar akalla mutane 600 suka jikkata sakamakon fashe-fashen nakiyoyin, baya ga wasu 20 da suka mutu, zalika akwai yiwuwar a samu karin adadin mamatan da kuma wadanda suka jikkata.

Hoton bidiyon dake nuna yadda mutane suka rika kai agajin gaggawar taimakawa wadanda fashe fashen sinadaran hada bama bamai ya rutsa da su.
Hoton bidiyon dake nuna yadda mutane suka rika kai agajin gaggawar taimakawa wadanda fashe fashen sinadaran hada bama bamai ya rutsa da su. AP

Hotunan bidiyo da kafafen talabijin na kasar ta Equatorial Guniea suka yada, sun nun yadda aka rika zaro mutane daga karkashin baraguzan gine-ginen da suka ruguje dalilin tarwatsewar nakiyoyin sansanin sojin na birnin Bata.

Katangun gidajen dake kusa da inda lamarin ya auku kalilan ne dai suka rage a tsaye saboda karfin fashe-fashen nakiiyoyin da suka tarwatse, wadanda suka girgiza hatta gine-ginen dake nesa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.