Burkina-Ta'addanci

Burkina Faso za ta fara tattaunawa da mayaka masu ikirarin jihadi

Wasu dakarun Sojin Burkina Faso a yakin da su ke da mayaka masu ikirarin jihadi a kan iyakar kasar.
Wasu dakarun Sojin Burkina Faso a yakin da su ke da mayaka masu ikirarin jihadi a kan iyakar kasar. The Washington Post via Getty Im - The Washington Post

Shugaban Burkina Faso Marc Christian Kabore ya fara nuna alamun yiwuwar tattaunawa da ‘yan ta’addan kasar masu ikirarin jihadi, bayan tun farko ya yi watsi da shirin magabacinsa Blaise Compaore da ke ganin tattaunawa da mayakan ne zai samar da zaman Lafiya a kasar mai fama da matsalar tattalin arziki.

Talla

Shugaba Roch Marc Christian Kabore ko a yakin neman zabensa cikin watan Nuwamba ya nanata cewa rashin azanci ne tattaunawa da mayakan masu ikirarin jihadi, yana mai cewa babu ta yadda za ayi gwamnatinsa ta amince da zama kan teburin sulhu da mayakan da ke sake wargaza zaman lafiyan kasar.

Sai dai kalaman Kabore ya yi hannun riga da na tsohon shugaban kasar Blaise Compaore da ke ganin zama teburin sulhu ne kadai zai warware rikicin ta’addancin kasar, bisa kafa hujja da cewa iyakar tattaunawar da aka fara da mayakan jihadin a Mali ya sassauta hare-haren da Burkina ke fuskanta.

Shugaba Kabore a wancan lokaci ya bayyana cewa kin amincewa da hawa teburin sulhun da ‘yan ta’addan na samun cikakken goyon bayan Faransa wadda yakinta da ta’addanci ke shiga shekara ta 9 da faraway a yankin na Sahel.

Wasu majiyoyi kamar yadda kamfanin dillancin labaran Faransa ya wallafa sun ruwaito cewa gwamnatin kasar ta fara tuntubar shugabancin mayakan jihadi a matakin yankuna ko da ya ke zuwa yanzu ba a tuntubi babbar kungiyar ta’addancin da ke biyayya ga IS ba.

Matakin yunkurin fara tattaunawa da mayakan jihadin a Burkina na zuwa bayan tun a watan Fabarairu Firaminista Christope Dabire ya bayyana cewa kusan kowanne rikici da ya kai tsanani teburin sulhu ne kadai ka iya warwareshi ba makamai ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.