Hukuncin dauri zuwa mutane 16 da aka sama da laifin kisa a DRCongo

Wasu jami'an Lafiya da ke shirin tunkarar aikin rigakafin na Ebola.
Wasu jami'an Lafiya da ke shirin tunkarar aikin rigakafin na Ebola. REUTERS/Baz Ratner/File Photo

Kotu a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo, ta yanke hukuncin kisa a kan mutane 16, wadanda ta sama da laifin kashe wani likita dan asalin kasar Kamaru da ke yaki da cutar Ebola karkashin Hukumar Lafiya ta Duniya a kasar ta Congo.

Talla

Daga cikin wadannan mutane da aka yanke wa hukuncin har da wani kwararren likita mai suna Dr Jean-Paul Mundama, sai kuma wasu mutane 15 da aka bayyana cewa ‘yan bindiga ne da aka sama da hannu wajen kashe Dr Richard Valery Mouzoko Kibong, dan asalin kasar Kamaru da ke aiki karkashin hukumar lafiya ta duniya.

Lamarin dai ya faru ne a shekara ta 2019, inda ‘yan bindiga suka bude wuta a kan likitan, a wani asibitin Ebola, a garin Butembo na lardin Kivu ta Arewa, inda annobar ta Ebola ta kashe mutane akalla dubu biyu da 200 tsakanin 2018-2020.

Bincike ya nuna cewa wani gungun jami’an kiwon lafiya ‘yan asalin kasar ta Congo ne suka tsara wannan kisa, saboda razana likitoci ‘yan asalin kasashen ketare masu yaki da wannan annoba domin su bar kasar.

Likitocin dai na zargin cewa ana nuna masu bambanci ta fannin albashi, yayin da ake biyan dan asalin kasar ta Congo dala 20 a rana, hukumar lafiya kuwa na biyan dala dubu 20 kowane wata a matsayin albashi ga likita dan asalin wata kasa ta ketare.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.