Libya

Dakarun Libya sun ceto 'yan ci rani 120 daga sansanonin azabtarwa

Wasu 'yan ci rani da suka tagayyara a Libya, yayin kokarin tsallakawa zuwa nahiyar Turai.
Wasu 'yan ci rani da suka tagayyara a Libya, yayin kokarin tsallakawa zuwa nahiyar Turai. ASSOCIATED PRESS - Abdel Magid al Fergany

Jami’an tsaron Libya sun ceto ‘yan ci rani 120 daga hannun kungiyoyi na masu safarar mutane da suka shafe lokaci mai tsawo suna tsare da su cikin azabtarwa.

Talla

Rundunar sojin Libya ta ce mafi akasarin ‘yan ci ranin da ta ceto daga wani sansanonin gungun masu safarar mutane dake arewa maso yammacin garin Bani Walid ‘yan kasar Masar ne.

Garin Bani Walid mai nisan kilomita 170 daga kudu maso yammacin birnin Tripoli, yayi kaurin suna a kasar Libya wajen zama cibiyar kungiyoyin masu safarar mutane gami da azabtar da su har ma kisan gilla a wasu lokutan.

Tun bayan barkewar rikici a 2011 bayan kashe tsohon shugaban Libya Mu’ammar Ghaddafi da masu bore suka yi tare da goton bayan rundunar sojojin NATO, kasar ta zama cibiyar da masu gudun hijira da ‘yan ci rani ke bi wajen tsallaka teku domin zuwa nahiyar Turai.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.