Afrika ta Kudu

Gwajin sabon maganin tarin fuka ya samu nasara a Afrika ta Kudu

Wani likita yayin nazari kan hoton kirjin wani mai fama da cutar tarin fuka ko TB a asibitin dake yankin Gugulethu na birnin Cape Town a Afrika ta Kudu. 9/11/2007.
Wani likita yayin nazari kan hoton kirjin wani mai fama da cutar tarin fuka ko TB a asibitin dake yankin Gugulethu na birnin Cape Town a Afrika ta Kudu. 9/11/2007. AP - Karin Schermbrucker

Wani bincike ya bayyana cewar kusan duk mutanen da suka karbi sabon maganin cutar tarin fuka ko TB dake bijirewa magunguna a gwajin da aka yi a kasar Afirka ta kudu sun rabu da cutar shekaru biyu bayan yin gwajin sa da akayi.

Talla

Babbar jami’ar da ta jagoranci binciken da aka gudanar kan wadanda suka karbi maganin, Dr Pauline Howell tace sabanin abinda aka gani shekaru 5 da suka gabata, kashi 80 na mutanen dake fama da cutar tarin fuka dake bijirewa magani mutuwa suke yi.

Sakamakon binciken da ba a kai ga wallafa shi ba tukuna, an gabatar da shi ne a wani taron masana cututtuka masu yaduwa da aka gudanar ta kafar bidiyo saboda illar cutar korona.

Gideon Mtongona yayin amsa tambayoyi daga Likita a asibitin kula da masu fama da cutar tarin fuka garin Langa dake Afrika ta Kudu. 17/3/2008.
Gideon Mtongona yayin amsa tambayoyi daga Likita a asibitin kula da masu fama da cutar tarin fuka garin Langa dake Afrika ta Kudu. 17/3/2008. ASSOCIATED PRESS - SCHALK VAN ZUYDAM
Howell tace wannan sabon magani ya warkar da akalla mutane 9 daga cikin kowanne 10 dake fama ad cutar, kuma abin farin ciki shine kowanne daga cikin su ya tabbatar da warkewar sa bayan kamala shan maganin.

Magungunan da ake amfani da su ada wajen yaki da cutar tarin fuka na haifar da matsalolin dake da nasaba da tabin kwakwalwa da kuma sauya fatar jikin mai fama da cutar.

Jami’ar tace ada mai fama da cutar kan kwashe shekaru 2 yana shan magungunan da suka kai kwayoyi 20,000 wanda ke iya illa ga mutane, sabanin wannan sabin maganin wanda za’a sha na watanni 6 kafin sanya ido akan mai fama da cutar na Karin watanni 6.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.