Afrika ta Kudu

Sarkin Zulu ya rasu a Afrika ta kudu

Kabilar Zulu a Afrika ta kudu,tareda Johnny Clegg bature da yake sha'awar al'adun Zulu.
Kabilar Zulu a Afrika ta kudu,tareda Johnny Clegg bature da yake sha'awar al'adun Zulu. AFP/File

Masarautar Zulu ta Afrika ta Kudu ta bada sanarwa rasuwa sarkin ta, Goodwill Zwelithini a yau Juma’a yana da shekaru 72, bayan shafe makonni a asibiti yana jinyar cutar siga.

Talla

Sarkin wanda aka haifa a Nongoma, wani karamin gari a kudu maso gabashin lardin Kwa-Zulu Natal, ya dare kan karagar mulki ne a shekarar 1971, a zamanin mulkin wariyar launin fata ta apartheid. 

A yayin mulkinsa na shekaru 50, Zwelithini ya farfado da bukuwan al’adun gargajiya da suka hada na jinjina wa matan da suka tsira da budurcinsu. A baya Sarkin Zulu da ke kasar Afirka ta kudu, Goodwill Zwelithini ya nesanta kansa da zargin tinzira al’ummar kasar su afkawa baki wajen kai musu hare hare, bayan zarginsa da rura wutar rikicin da ya janyo asarar rayukan akalla mutane bakwai a cikin wannan kasa.

Afrika ta kudu ta yi kaurin suna wajen kyamar baki musaman a yan shekaru nan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.