An dakatar da shirin yiwa mutane allurar Covid 19 a DRCongo
Wallafawa ranar:
Ministan kiwon lafiyar Jamhuriyar Demokkuraddiyar Congo a yau asabar ya sanar da dakatar da allura da aka shirya yiwa mutan kasar dangane da rigakafi da cutar Covid 19.
Ta bakin jami’in gwamnatin, an shirya yiwa jama’a allurar ne kama daga ranar 15 ga wannan watan da muke cikin sa, an dai shigo da kusan allurai na AstraZeneca milyan daya da dubu dari 7.Daukar wannan mataki a cewar jami’in na zuwa ne yan lokuta bayan da wasu rahotanni daga kasashen ketare ke nuna wasu matsalloli da ake fuskanta bayan yiwa mutane wannan allura.A karshe Ministan ya bayyana cewa nan gaba ,hukumomin kasar za su sanar da ranar da ta dace an soma yiwa jama’a wannan alura.Hukumar lafiya ta duniya ta ce babu wani abin da zai sa a dakatar da bada rigakafin Covid-19 ta AstraZeneca bayan da kasashe da dama suka sanar da daina amfani da shi sakamakon fargabar cewa yana haddasa dunkulewar jini, a yayin da Amurka, wadda cutar ta fi yi wa ta’adi ta kai ga yi wa mutane miliyan 100 allurar rigakafin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu