Tanzania-Coronavirus

Hukumomin Tanzania sun ce shugaba Magafuli yana cikin koshin lafiya

John Pombe Magufuli Shugaban kasar Tanzania
John Pombe Magufuli Shugaban kasar Tanzania REUTERS/Sadi Said

Hukumomin Tanzania sun ce shugaba John Magufuli yana cikin koshin lafiya, biyo bayan rahotannin da ke cewa an garzaya da shi asibiti a wata kasar waje, sakamakon harbuwa da Korona.

Talla

Magufuli mai shekaru 61 wanda ya yi fice wajen bayyana kokwanto a game da wanzuwar cutar covid 19, ya bace daga bainar jama’a tun ranar 27 ga watan Fabrairu.

Jagoran ‘yan adawan kasar Tundu Lissu, ya ce shugaba Magafuli ya kamu da cutar Korona ne, kuma an kai shi wani asibiti mai zaman kansa a birnin Nairobin Kenya, daga nan aka garzaya da shi India ciin halin rai-kwakwai-mutu-kwakwai.

Sai dai Fira ministan kasar, Kassim Majaliwa  ya musanta labarin, yana mai zargin wadanda ya kira “‘yan Tanzania makiya” da ke zama a kasashen waje da yada labarin kanzon kurege.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.