HWR ta bukaci a gudanar da bincike kan kisan masu zanga-zanga a Senegal
Wallafawa ranar:
Kungiyar kare hakkin dan adam ta Human Rights Watch ta bukaci Senegal ta kaddamar da wani bincike mai zaman kansa a game da mutuwar masu zanga-zanga a yayin tarzomar da ta barke a kasar a makon da ya gabata.
Akalla mutane 5 ne suka mutu a rikice rikicen da aka samu a sassan kasar bayan hatsaniyar da aka samu a ranar 3 ga watan Maris a lokacin da ‘yan sanda suka kama jagoran adawan kasar Ousmane Sonko.
Rikicin ya ci gaba har zuwa ranar 8 ga watan Maris, kuma an samu sabanin alkalumma a game da yawan wadanda suka mutu.
Wata kungiyar adawa a Senegal ta soke zanga zangar da ta shirya yi a yau Asabar bayan wadda aka gudanar tun da farko a kan kame sonko ya janyo tarzoma a sassan kasar.
Hadakar mai ikirarin kare dimokaradiyya da ake Movement for Defence of Democracy, ta bayyana a wata sanarwa jiya Juma’a cewa ta dage wannan zanga-zangar da ta shirya gudanarwa har sai yanda hali ya yi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu