Idris Deby ya kaddamar da yakin neman zaben wa’adi na 6
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Shugaban kasar Chadi Idris Deby Itno dake neman wa’adi na 6 ya kaddamar da yaki neman zaben sa yau asabar wanda ya samu halartar dubban magoya bayan sa a birnin N’djamena.Wannan shine karo na farko da shugaban ya kaddamar da yakin neman zaben wanda a hukumance aka fara shi a ranar alhamis da ta gabata.
Rahotanni sun ce magoya bayan Jam‘iyyar sa ta MPS sun cika filin wasan da aka sanya masa sunan Idriss Mahamat Ouya mai daukar mutane 15,000 a babban birnin kasar.
Shaidun gani da ido sun ce magoya bayan shugaban sanye da rigunan dake nuna tutar Jam’iyyar su sun yi gangamin ba tare da sanya kyallen rufe baki da hanci ba.
Shugaba Deby da uwargidan sa Hinda sun shiga filin wasan cikin matakan tsaro domin kare lafiyar su, yayin da ya shaidawa gangamin cewar ya kwashe shekaru 30 yana yakin hada kan jama’ar kasar domin tabbatar da zaman tare da kuma gudanar da harkokin su cikin lumana.
Yan adawar kasar na zargin shugaban da amfani da karfin mulki wajen murkushe su da kuma hana su gudanar da yakin neman zabe.
Kotun kolin kasar ta haramtawa wasu daga cikin Yan adawar tsayawa takara, yayin da wasu kuma suka janye, inda suka zargi shugaban da amfani da karfi wajen hana su gudanar da harkokin su.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu