China ta taimakawa Gabon da alluran rigakafin Covid-19
Wallafawa ranar:
Kasar China ta taimakawa Gabon da alluran rigakafin cutar covid 19 dubu 100 da kamfanin hada maguguna na kasar Sinopharm ya hada.Shugaban kasar ta shafin san a Facebook ya bayyana cewa za a soma yiwa jami’an kiwon lafiya,jami’an tsaro da tsofin wannan allura, da hukumomin China suka tabbatar da ingancin ta da kusan kashi 79 cikin dari.
A kasar ta Gabon yanzu haka kusan mutane dubu 16.660 ne suka kamu da cutar,yayinda 96 suka mutu bayan harbuwa da kwayar cutar tun bayan da da ta bulu.
Makwabciyar Gabon Equatorial Guinne ta mori alluran dubu 100 daga kasar China da kamfanin Sinophar ya samar,wanda hakan zai kuma taimaka don takaita yaduwar cutar a fadin kasar,wacce aka kuma soma yiwa jama’a allurar tun ranar 14 ga watan Fabrairun shekarar bana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu