Guinea - Ebola

Mutanen da suka warke daga Ebola ne suka sake yada ta Guinea - WHO

Magidanci Kissi Dembadouno daga tsakiya, yayin da 'yan uwansa ke masa jajen mutuwar matarsa da 'yarsa sakamakon kamuwa da cutar Ebola, a kauyen Meliandou dake kasar Guinea.
Magidanci Kissi Dembadouno daga tsakiya, yayin da 'yan uwansa ke masa jajen mutuwar matarsa da 'yarsa sakamakon kamuwa da cutar Ebola, a kauyen Meliandou dake kasar Guinea. AP - Jerome Delay

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce akwai alamun da ke nuna annobar Ebolar da ta sake barkewa yanzu haka a Guinea ta yadu ne daga jikin wadanda suka kamu a baya, sabanin yadda aka saba ganin barkewarta daga wasu halittu zuwa mutum a shekarun baya.

Talla

Akalla sabbin kamuwa da Ebola 18 aka samu a Guinea cikin shekarar nan, karon farko da kasar ke ganin bullar cutar tun bayan wadda aka yi fama da ita daga 2013 zuwa 2016 dake matsayin mafi munin annoba da kasar ta gani wadda ta kashe dubban jama’a.

Babban jami’in sashin gaggawa na WHO Mike Ryan, ya shaidawa taron manema labarai a Geneva cewa, abu ne mai matukar mamaki yadda cutar ta bayar da tazarar lokaci tun daga 2016 kana ta ci gaba da yaduwa a yanzu, ko da yake ya bukaci tsananta bincike.

MIke Ryan mataimakin darakatan hukumar WHO kan ayyukan gaggawa.
MIke Ryan mataimakin darakatan hukumar WHO kan ayyukan gaggawa. AP - Salvatore Di Nolfi

Mike Ryan ya ce iyakar bincikensu a yanzu na nuna cewa cutar tun a wanan lokaci ta makale a wani sashi na jikin dan adam daga bisani kuma ta cigaba da yaduwa.

Sai dai kalaman wani babban jami’in hukumar na daban a taron manema labaran, ya ce akwai bukatar karin lokaci kafin fitar da sakamakon karshe kan ta inda cutar ta bullo a wannan karon.

Cutar Ebola dake saurin kashe dan adam, galibi an fi samun bullarta ta hanyar yaduwa daga jikin ko dai biri ko kuma jemage kamar yadda WHO ke sanarwa a baya, ko da yake hukumar ta ce kwayar cutar kan iya makalewa a wani sashi na jikin wani da ya yi fama da ita na tsawon lokaci ba tare da ta nuna ba kana ta sake fantsama a wani lokaci na daban.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.