Nijar-Najeriya

Jamhuriyar Nijar na shirin rage dogaro da Najeriya a fannin lantarki

Babbar tashar lantarkin Najeriya da ke baiwa kasashen Nijar da Benin haske.
Babbar tashar lantarkin Najeriya da ke baiwa kasashen Nijar da Benin haske. AFP/File

Jamhuriyyar Nijar ta kaddamar da wani gagarumin aikin samar da wutar lantarki a birnin Yammai wanda ake ganin zai taimaka mata wajen rage dogaro da Najeriya.

Talla

Tashar samar da megawatt 89 na wutar an tsara shi ne domin baiwa birnin Yammai da kudancin Dosso da kuma Tillaberi wutar duk lokacin da aka samu matsala daga Najeriya.

Shugaban kasa mai barin gado Mahamadou Issofou ya jagoranci kaddamar da aikin a daidai lokacin da yake kawo karshen wa’adin sa biyu na shekaru 10.

Ko a shekarar 2017 gwamnatin sa ta bude wata tashar samar da wutar lantarki mai amfani da man gas amma daga baya ta fuskanci matsaloli.

Sabuwar tashar da ta lakume Dala miliyan 120 a karkashin shirin hadin kai tsakanin gwamnatin kasar da wani kamfanin kasar Mauritania da ake kira Istithmar West Afrika.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.